Wata Babbar kirista ta karbi Musulunci

Babbar Fasto A Katsina Ta Jingine Kiristanci Ta Rungumi Musulunci.

Jaridar Sarauniya ta buga a shafinta cewa “Fasto a jihar Katsina Grace Aji ta jingine addinin Kiristanci ta rungumi addinin Musulunci. Faston ta sauya sunan ta zuwa Hauwa’u. A cewarta ta yi matukar godiya ga Madaukakin Sarki Allah da ya Shiryar da ita ga tafarkin addinin Musulunci.” Sai dai jaridar bata bayyana ko a wane karamar hukama acikin jahar haka  yafaru ba.

GWAMNATI NA SHIRYE SHIRYEN KADDAMARDA TASHAR JIGIN RUWA

Gwannatin Nageria na Shirin kaddamar da sabuwar tashar jirgin ruwa ta zamani a garin baro acikin karamar hukumar Agaye a jahar Niger. Idan kun tuna cewa marigayi tsohon shugaban kasa Alhaji Ummaru Musa Yar’aduwa lokacin mulkinsa yabayar da aikin yashe tekun inda jirgin ruwa zaizo har arewa, amma bayan wafatinsa gwannatin data biyo baya da dakile kokuma ta chaza alkiblar aikin.

Amma kamar yadda zaku kalla kuma ku saura ra a wannan bidiyo dake sama cewa gwamnati a kar kashin shugabancin Muhammadu Buhari shekaru ukku baya ta sake bayarda aikin, wanda kuma ake ganin cewa haka ta kusa cimma ruwa, shugan hukumar kula da hanyoyin jiragen ruwa Alhaji Danladi Ibrahim ne ya bayyana hakan inda yake cewa tuni aka kammala aikin kuma aka hada ta da tasha ta jirgin kasa, an sayo na’urori na zamani inda ake shirin kaddamar da ita a watan Augustin.

Zaku iya tunawa kwanakin baya shugaba muhammadu Buhari ya kaddamar da wata tashar ta tudu a kaduna da kuma shirin kafa ire iren su da dama a fadin kasar nan.